<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Hughes, John (1873-1932), Williams, William (1717-1791)</author>
<lyrics>[V1]
 1) Ga mai shibka cikin gona
 Yana watse irinsa
 Wasu su ka faɗi akan hanya
 Tsuntsaye suna cinyewa.

[V2]
 Kaka Mugun ya fige daga zuciya
 Maganar Allah da akan shibka.

[V3]
 2) Cikin marmara wasu sun faɗi
 Inda ba su da ƙasa ba
 Amma rana ta ƙone su
 Tun ba su da sayu ba.

[V4]
 Haka tsanani ko da ƙunci
 Shi kan sa mutum shi tun tuɓe.

[V5]
 3)Wasu cikin ƙaya sun faɗi
 Ҡaya su kan shake su
 Haka ruɗin dukiya  ta duniya
 Ta kan maida shi mara amfani.

[V6]
 Wanda shi kan ji, shi maida hankali
 Irin shibka da a ke yi.

[V7]
 4) Bisa ƙasa mai kyau wasu sun faɗi
 Su kan bada amfani
 Haka wanda ya saurara ya gane
 Har ya karɓi da zuciya ɗaya.

[V8]
 Riɓi talatin, wasu sittin
 Har wasu sun kai ga ɗari.</lyrics>
<title>Ga Mai Shibka Cikin Gona LW411</title>
<hymn_number>411</hymn_number>
</song>